Jihar Kano - Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) ta damƙe wata mata ɗauƙe da ƙunshin hodar iblis 52 a filin sauka da tashin jiragen sama na Aminu Kano a jihar Kano.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa NDLEA ta kama matar mai suna, Bilkisu Mohammed Bello, yayin da take yunkurin kama jirgi zuwa ƙasar Saudiyya.
A wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai na hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar, ya ce jami'ai sun cafke matar da ake zargin ne tun ranar Talata.
"A yayin da ake zantawa da ita, ta amsa cewa kwalayen hodar iblis da aka ba ta ta hadiye kafin lokacin tashin jirgin nata an ajiye su ne a wani gida da ke unguwar Farawa a Kano."
"Lokacin da ta jagoranci jami'an hukumar NDLEA zuwa gidan, an samu ƙunshi 52 na haramtattun kayan da nauyinsu ya kai giram 767."
No comments:
Post a Comment