Sabuwa rikici ya ɓarke tsakanin Maryam kk wanda ake kira autar 13×13 da Aisha Humaira rikicin ya samu asali ne tun lokacin da jaruma Aisha Humaira tayi magana akan mata su daina yin ciko domin ciko yana jawa mata matsala sun dan gana domin kuwa duk wanda Allah ya baiwa gaba da kirji sune asalin da shi..
Aisha Humaira tayi maganar ne cewa yin ciko yana da illa musaman a jikin lafiyar su da kuma idan mutum yaganki da ciko ya aureki to tabbas kinka tare ya gane gaskiyar zance za’a samu matsala, to anyi sara bisa gaɓa ne domin a daidai lokacin jaruma samha m inuwa da kuma maryam kk sunkayi tallar wani kamfanin atampa dukansu sunka dauka da zafi.
Maryam kk a lokacin ta fito tayi maganganu da dama ganin mutane suna daukar da su take amma duk da hakan A’isha Humaira bata yi magana ko daukar mataki ba.
To matsalar da ta tayar da wannan husuma shine ta fito a shafinta na tiktok live sai anka samu wasu mutane a ƙarƙashin live din ana martani “comments section” kenan suna rubuta cewa tayi butulci tayiwa Rarara da A’isha Humaira butulci domin sunyi mata riga da wando.
A nan ne ita kuma abun yayi mata zafi ita maryam kk tayi musu kuɗin goro ta zage masu rubuta martani da kuma ita jaruma Aisha Humaira abokiyar aikin Dauda kahutu Rarara.
Amma a wannan mataki aisha Humaira bata iya jure wannan zagi da cin zarafin da maryam kk tayi mata.
A dalilin hakane ita Aisha Humaira taga wannan yarinyar wuyanta yayi kwari bari ta dauki mataki inda nan take ta yanko mata sammace wanda abun kafin aje can, shugabani da manya da ke Masana’atar kannywood din sunka baiwa ita Aisha Humaira hakuri ta jane maganar ƙarar da ta shigar tsakaninta da Maryam kk kuma ta hakura. majiyarmu ta samu wannan labarin daga sharin YouTube mai suna Hausa media
Wannan shine asalin abinda ya sanya aisha Humaira kai karar Maryam kk da anka fi sani da autar 13×13 da yayi mata ba dadi .
Amma Alhamdulillahi ta janye tayi hakuri amma ta gindaya sharudda wanda duk zaku gansu a Cikin abinda ta wallafa.
Bayan shigar manya cikin lamarin itama maryam kk ta wallafa hotunta tare da Aisha Humaira a shafinta na Instagram ida take cewa.
“Duk abinda kika mun na yafe miki duniya da lahira Ina godiya ga manyan da suka min magana kuma suka min fada Sannan suka ce min na dubi zaman da nayi da mutum a baya sai alkhairi sa ya wanke sharrin sa Nagode sosai Allah ya saka muku da alkhairi
#kannywood”
No comments:
Post a Comment