Idan baku manta ba babban malamin addini shekh Pantami yana daya daga cikin manyan malaman addini wanda ake dasu a fadin duniya bama nijeriya ba kadai wannan babban malami ya koka bayan cin karo da yake da wasu bidiyoyin musulmai hausawa a online da suke daurawa.
Malam yana cewa “Yara suna tsalle suna nuna tsaraicin jikin su a online ana kallo kuma a gidan iyayen su suke wannan, shi uba yana tunanin yarinyarsa ta waye, shin wutar da ake magana wasa ce, shin kuma tunanin Allah yana wasa damu ne.”
Ya cigaba da cewa “An wayi gari a al’ada ka kasa gane ina musulmi yake da wanda ba musulmi ba, idan aka sanya kaya ka kasa ganewa a mu’amala ka gagara ganewa, kuma a haka muna karanta Alqur’ani.”
Wannan itace takaitacciyar nasiha da malam yayi kan irin lalatar da shigar yan wuta da matan wannan zamani suke iyayen su na kallo kuru kuru, a matsayin yaransu sun waye.
A cikin maganar sa yayi amfani da kuma ganin wutar nan wasa ce, ma’ana bakuyi imani da akwai wuta ba kuma duk wanda baiyi imani da abinda Allah yace akwai ba, shi ba musulmi bane yana amsa sunan musulunci ne kawai.
Ga bidiyon da malam yayi yar takaitacciyar nasiha:
No comments:
Post a Comment