Abba Gida-Gida wanda ya sanar da hakan a Fadar Gwamnatin Kano ya ce zai aurar da jarumar ce a cikin zawarawan da gwamnatinsa ke shirin aurarwa kwanan nan.
Gwamnan ya ce zai yi wa Murja wannan tagomashi ne la’akari da gudunmawar da ta rika bai wa gwamnatinsa tun gabanin ya lashe zaben da aka yi a watan Maris, har zuwa yanzu.
A cewarsa, “kowa ya san irin rawar da Murja ta taka wajen yayata ayyukan alheri da gwamnatin nan ke yi, wanda babu abin da za mu ce sai son barka.
Kuma ita ce ta fara fitowa a cikin ’yan group dinsu [’yan TikTok] ta ce tana son a yi mata aure sunnar Manzon Allah.
“Matar da ta fito ta ce tana son a inganta sunna ta Manzon Allah ai ba a bar kyama ce.
“Kuma so take ta je inda za ta ba da gudunmawar inganta addinin Musulunci.”
No comments:
Post a Comment