Fitacciyar jarumar Kannywood Aisha Humaira ta bayyana rashin jin dadinta a kan wani taimako da ta ce ta yi amma yanzu ya zame mata karfen kafa.
Jarumar ta ce yaron da yayi takakkiya har zuwa Kano daga Bauchi don ganinta ta yi masa goma ta arziki har da mahaifiyarsa, ta kuma yi alkawarin mayar da shi makaranta don ci gaba da karatunsa. bayan ta sa na mayar da shi Bauchi sau biyu.
Yanzu dai Hisba ta shiga tsakani, amma duk da haka ya sake komawa wajen jarumar a karo na 3. Yaro ya kafe shi sai wajen Aisha Humaira zai zauna.
Aisha Humaira na kira ga hukumomin da iyayen yaran da su taimaka su rabata da shi.
Idan bazaku manta ba mun kawo muku rahoto haduwarsu da jaruma Aisha Humaira da yaron harda mahaifinsa amma yanzu abinda hausawa kance ganwo ya birkice da dame.
No comments:
Post a Comment