Wata Matashiya a Najeriya ta bayyana irin halin da wata kawarta ya shiga bayan wani damfarar kalamai da wani saurayi ya yi mata lokacin suna nema.
Matashiyar mai suna Fairy Gbemie ta bayyana cewa mijin kawar tata ya sharara mata karyar cewa shi dillalin motoci ne, to amma bayan sun yi aure ta gane cewa ashe Makanike ne.
Ko da yake bata bayyana sunan kawar tata ba, amma bisa la'akari da Kalamanta ta nuna cewa yana zirga-zirga cikin motoci daban-daban lokacin da yake zuwa wurin ta
Duk da cewa har kawo yanzu ba ta bayyana tsawon lokacin da suka shafe a tare ba, amma galibin jama'a na hasashen cewa wannan aure ba lallai ne ya yi karko ba.
Da ma dai a irin wannan zamani yan mata da dama na kasancewa ne a sahun ma'abota samun wurin hutu a rayuwarsu ta aure, to amma an ce tabbas idan da kwadayi lallai akwai wulakanci.
No comments:
Post a Comment