Breaking

Quote of the day

Quote of the Day

Pages

Search here

Thursday, 24 August 2023

Ali Nuhu ya bayyana wanda yafi jin daɗin fim da shi

Gidan jaridar Dwhausa da kasar jamus suna wani shiri da suke kira Nasarata a Masana’atar Kannywood wanda sunka samu zantawa da babban jarumin Ali Nuhu.

Shirin nasarata shiri da bakon shirin zai fadi takaitaccen labarin rayuwarsa daga nan sai a cigaba da tsuduma irin nasarori da kuma kalubali da ya samu a rayuwarsa.


Ali Nuhu ya fadi cewa shi cikakken faifan Maiduguri ne jihar barno amma kuma shi asalin sa shine jihar Gombe domin daga can ne mahaifiyansa ya fito.

Ali Nuhu ya bayyana cewa a farkon harka fim dinsa rubuta fim ne ya fara yi kafin ya fara fitowa jarumi har yayi suna sosai a duniya a ɓangaren kannywood amma a ɓangaren fina finai na kudu yace fim da ya fara yi shine wanda sunkaje jos ga sanyi ana ruwa kuma a lokacin an haifi Ahmad dansa to fim din zai fito a matsayin musulmi daga arewa su kuma sauran zasu sanya walki ne to ya sha wahala sosai a fim din.

Mai tambaya yayi masa tambaya game da shin wanene ko su waye kafi jin dadin aiki ma’ana fim da su.

Shine Ali Nuhu ya amsa da cewa ga amasar nan:

“Gaskiyar magana shine duk lokacin da nake son yin fim musamman yanzu zanyi a kamfanina ko wani abu akwai mutum biyu ina aiki da su yadda abun yake ko yadda na gayamusu a rubuce to zanga sun bada shi ba tare da na sha wahala ba. Adam a Zango da shuaibu lawan kumurchi in ina aiki da su gani nake kamar ni da kai nane nake yi ba wani bane ake sawa ba.”

Ku saurari cikakken hirar a nan.




No comments:

Post a Comment