Wani mahalifi ya daddatsa dan cikinsa a Jihar Akwa Ibom, bayan ya zarge shi da hakar masa rogo a gona ba tare da izini ba jaridar Aminiya na ruwaito.
Ana zargin mutumin mai suna cif Akpan Aniekan da daddatsa dan nasa mai suna Boniface Innocent Uko mai shekara 26 mazaunin kauyen Ebe Ikpe a Karamar Hukumar Essein Udim, da daddatsa dan nasa ne da adda.
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar, SP Odiko Macdon, ya ce bayan kashe dan nasa, mutumin ya kuma kone gawar sannan ya saka ta a cikin masai domin ya bad da sahu.
Sai dai Kakakin ya ce bayan an kama mutumin, ya amsa aikata laifin, inda ya ce ya yi hakan ne saboda munanan dabi’un dan nasa da kuma jawo masa abin kunya.
Kakakin ya kuma ce ofishinsu da ke Uruan, ya kama wani mutum mai suna Edem John, da ake zargi da sace wasu yara su biyu masu shekara bakwai-bakwai.
Ya ce dakarun rundunarsu sun sami nasarar kama mutanen ne bayan wasu rahotannin sirri da suka samu.
No comments:
Post a Comment