Kasancewar jiya naga wasu suna fadin kamar a novel ko ya muke handling matsalar mu in mun samu problem.
Nafarko dai rayuwar auren mu kamar ko wani aure ne, muna da matsaloli da qalubalen da tun shekaran farko na aure har zuwa yau muna fuskantansu, muna da jarrabawar da muke fama dashi har yanzu, muna da banbancin dake tsakanin mu, muna da weakness din mu, muna da negative dabi’un da dukkan mu muke hakuri da kawaici akan juna.
Sai dai Alhamdulillah da agaji da taimakon Allah mun kiyaye kuma mun qi mu bari wadannan abubuwa suyi tasiri a cikin zamantakewar auren mu da zai zama sanadin rashin zaman lafiyar mu. Mun kasance mukan kalli alkhairen juna fiye da kallon sharrin juna, muna hakuri da juna gwargwadon hali, in muka samu matsala bamu cika barinta ta dau lokaci bamu shirya ba asalima duk fushi da tutsun baya wuce ‘yan awanni zuwa kwana 1-2 tsanani 3 nan za muyi welcome back mu cigaba daga in da muka tsaya.
Tun da mukayi aure kowa yasan role da responsibility din sa a cikin auren, ni na ajiye kaina inda Allah ya ajiye ni, shi ya dauki kanka in da Allah ya daukaka shi. Na dauki mijina gatana kuma abun rufin asirina duk da lokacin da mukayi aure shekarun sa biyu da soma aikin gomnati wadda salary sa a lokacin was 18k, amma ban taba rena abunda ya min ko yakeyi a gidan sa ba, ko in sa hankali akan abunda wasu ke samu da bana samu a gidan sa ba, bai taɓa yin wani dawainiya a gidan sa na rena ko nace yamin qaɗan ko ba irin abun nake so ba, asalima nakan bashi damar zaɓi akan abunda yaga zai iyayi, shi kuma bai taba gazawa wajen nuna himma dan ganin ya rufa mana asiri dai dai abunda Allah ya hore masa a lokacin ba, duk abunda yayi nakan amsa cikin farin ciki, yabo da godiya wadda har gobe inayi.
Duk da a lokacin ina da damar da zan iya nemo kudi ko tallafi wajen iyayena amma wallahil azeem ban taba masa complain irin rayuwar da muke ciki ba, kuma ban taba zuwa gidan kowa nemo taimako ba dan bana son abunda zai zubar masa da kima ko a ga gazawar sa ko in sa yaji ya gaza wajen lura dani a matsayin sa na shugaba kuma jagorar rayuwar mu.
Shi kuwa bai taba kashe zuciya ya zama cima zaune ko ya zama dan maula ko yana da shi yaki yima iyalan sa ba, samm, yasan hakkin da ya rataya a wuyan sa na iyalan sa da yana dashi ba bai dashi zai yi qoqari yaga ya tsira da mutuncin sa a idon iyalan sa. ( wannan dabi’ar yasa nake ganin sa a matsayin jarumi kuma cikkaken namiji dan yana aiki da hankali, ilimi da karfin da Allah ya masa wajen lura da hakkin iyalan sa).
Tun farkon auren mu nakan bashi dukkan girmamawa da ya chanchance shi, nakan masa biyayyar da har gobe yana iya sani ko ya hanani in hanu ba musu ko son jin dalili, ina tuna wani lokaci duk randa na fita nakan bi gidan mu ba tare da na tambaye shi ba, ni a tunanina bakomi, ashe abun baya masa dadi, ranar yace na hanaki sake zuwa gidan ku sai ran da nace ko kika tambaya, haka ba musu ko faɗa nace “toh”, ban sake zuwa gidan mu ko tambaya zuwa ba har sai randa ya yi ra’ayin sa shi da kan sa ya bani damar zuwa, wani lokaci har shike cemin kin kwana 2 baki leƙa gidan ku ba, ko yace ance Chief (Baba) ya zo kije ki gaishe shi.
Nakan nemi izini da amincewar sa a kusan dukkan abunda zanyi, hatta classes na abinci banayi ba tare da neman amincewar sa, ko kwanaki na nema ya bani izini, wani abu ya taso, hace in hakura, har na mayar ma wasu kudin da suka biya, amma da ikon Allah na samu abunda ko shakara zanyi ina wanan class din bazan samu abunda na samu ba. Ko wannan post din sai da na nemi izinin sa yace sai ya karanta kafun inyi posting.
Yakan nuna iko da isan sa akan wasu abubuwan amma basa damuna dan nasan mijina ne kuma ya isa ya nuna wanan isa da ikon akai na kuma a zauna lafiya, bana bijire masa in naga yana wannan abun ko inji haushi dan nasan namiji ne, akwai lokutan da ji da nuna wannan isar ne yake tabbatar musu da sun isa kuma sune jagoran tafiyar( ɗabi’a na kusan dukkan mazane).
Bana shiga harkan kudin sa, nawa ya samu, ya zan karɓi rabona ko in masa chuwa- chuwa, ko in damfareshi, ko wa yakema dawainiya ko nawa yake kashe ma kansa ko abunda yake saya da kudin sa, matuqar yana sauke hakkin daya rataya akan sa ban da matsala akai, kudin sane, shiya nemo abunsa so yana da ikon yin abunda ya ga dama da shi.
Akwai abubuwan da nasan yana hakuri dani akan su kamar yadda yasan akwai abubuwan da nake hakuri a kan sa.
Mukan bama juna lokaci, in muna da mtsala mukan zauna mu tattauna mu fahimci juna, kowa yakan amshi laifinsa a inda yayi kuskure ya kuma bada hakuri.
Duk abunda yake so ina matuqar kiyaye yin sa dan nasan shi ne zaman lafiya da ko wani namiji, bai ya son ganin bacin raina dan yasan gidan baya dadi in ina tutsu( na iya bori da tutsu harda style irin na kowace mace).
Mukan kyautata zato ga junan mu, mukan karfafi juna a inda muka fahimci daya na buqatar karfafa( emotional, mental and financial support).
A kullum mukan nemi tsari, taimako da agajin Allah a cikin zaman takewar mu dan mun san Shi ne kadai yake da ikon wanzar da zaman lafiya da jin dadi a rayuwar bayin Sa.
Rayuwar auren mu irin ta kowa ce dake tattare da irin nata qalubale, jarrabawa da duk wani up dan down da ba’a raba bawa da ita a rayuwa, banbancin kawai kowa da irin yadda ya fahimci rayuwar aure, ya dauketa kuma yake son yayita ko yakeyinta.
Mu dai mun dauketa in bamu gyara ba ba mai gyara mana, in bamu zauna lafiya ba, bamai zaunar damu lafiya, in bamu fahimci juna ba bamai fahimtar damu junan mu, in bamuyi hakuri da juna ba bamai yi mana, shiyasa a kullum muke neman agaji da taimakon Allah wajen ganin mun samu fahimta da zaman lafiya a tsakanin mu, Domin mun san ba iyawa, jimawa, ko qoqarin mu bane ya samar mana da wannan ni’imar, kyauta da rahamace daga Allah.
Daga karshe ina mai godiya ga dukkan addu’oin da fatan alkhairi da ku ka mana da mijina. Allah ya baku fiye da abunda kuka roqa mana.
No comments:
Post a Comment