Babban daraktan nan kuma naj mai baiwa gwamna shawara na musamman Sanusi oscar 442 yana zargin hukumar tace fina finai ta jihar kano inda ya wallafa wata waka da rubutu a jikinta inda yake cewa :
“Nifa ina zargin Dokar da hukumar tace finafinai tayi anfani da ita aka daure ni aka daure sadiq zazzabi aka daure naziru sarkin waka da kosan waqa ta daina anfani.”
Wanda yayi wannan wakar ana kiransa dan dan zaki mawakin Dan majalisar tarraya ne alhassan ado doguwa da kuma Dr. Abdullahi Umar Ganduje shugaban jam’iyyar Apc na kasa.
Ita wannan wakar da mai baiwa shawara na musamman a kannywood darakta sanusu oscar 442 ya wallafa anyiwa Dr Abdullahi Umar Ganduje ne inda ake suka da cin mutuncin mai gidansu Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.
Nan take mutane sunyi martani sosai a karkashin wannan fustin da mai bada shawara na musamman yayi inda kuma tattaro muku kada daga ciki.
@Umar bala2 cewa yake:
Shifa dauri ba haka kawai akeyinshi ba har sai an tanadi shaida, a ynz kuma bakuda wata shaidar wadda zaku iya daure mutum dan kawai yace tsula, domin bai kama sunan wanda kuke tunanin cewa dashi yake bah, Sbd hakan kuci gaba da hakuri kawai komai zaizo ya wuce.
@official_muhammad_sani cewa yake :
@ummarbala2 ka manata cewa a gwamnatin baya haka aka dunga daurin ba tare da hujja kwakkwara ba, ku dinga yiwa kanku adalci mana idan haka ne me Naziru Sarkin waka yayi lokacin da gwamnatin ganduje ta kamashi, ko me yayi baikai wanda wa’yannan mutanen sukeyi a yanzu ba, kiri_-kiri suke fitowa suna nuna ga da wanda suke zagi, ya kamata a fara ɗauke ko mutun 2 ne domin ragowar suji tsoro.
@kwankwason Instagram cewa yake : Mai zai hana Oscar ya ƙwaci hukumar tace fina-finai ta ƙarfin tsiya tunda yana ganin babu wanda ya iya sai shi
Wai dan Allah me Abba El-Mustapah ya tarewa mutanen nan ne, bawan Allahn da ko wata ɗaya baiyi a hukumar ba, kun dage lallai sai kun nuna bai iya ba?
To dan Allah ku ƙwaci kujerar nan ku bawa shi Kwale-Kwalen da kuke so a bawa dan ku ji daɗin juya shi yadda kuke so.
@mubara m muhmd cewa yake :
Wani lokaci sai ana kauda kai da wasu abubuwa domin shi babba inji hausawa sunce juji ne komi aka dauko akan kai cikinsa ne domin neman matsuguni su hakan da sukeyi neman matsuguni sukeyi to amma duk wanda yace da cin mutunci xe nemi abinci babu inda xeje wan nn ma alamace ta nasara ga jagora munada yan siyasa da dama a qasarnan amma shi kadai ne ya tsole musu ido lungu da saqo duk inda kashiga sakaji shi kawai ake magana to kaga wan nn ma nasarace me girma nidai a gani na wan nn ba kamu bane dai dai dasu Jan kunne ne kokuma a xura musu na mujiya domin kuwa shiru ma magana ce amma mutum yarinqa taka tsan tsan domin kuwa idan yashigo gonar mu he he he yasin jikin tabaro xeyi la’asar.
@kwankwasiya dubai 2 cewa yake : Kosan waka har katisna aka bishi aka kamashi dan yace a wanki gara @sunusi_oscar__442 gaskiya ka fada.
@kanywood22 cewa yake:
Idan ku an daureku a bisa zalunci to sukuma bazamuso a dauresu a bisa zalunci ba domin kuwa ba,a gyara barna da barna kudai a an zalunce ku to Allah yasaka muku kawai amma cigaba da aikata irin abinda akai muku ai ci bayane
No comments:
Post a Comment