Sheikh Ahmad Yusuf Guruntum yayiwa masu shirin “Mata A Yau” yayi kacaca da wankin babban bargo a tsakiyar kasuwa mallam ya fusata sosai akan wannan maganar ta gaisar da miji da ake ta dambarwa
Ko a garin mahaukata karya ne ace da wanda ake shugaban ta da wanda yake shugaba power su daya, karya ne ba’a tabayi ba.
Kuma ko a cikin dabbobi akwai shugaba akwai wanda ake shugabanta.
A makaranta akwai monitor wanda dalibi ne dan uwansa yayi surutu zai iya rubuta suna shi, kai ka isa ka rubuta sunan monitor ka bayar kaga wannan shugabanci ne anka bashi a cikin aji wanda ba’a baiwa sauran ba.
Head master yana iya tsayawa makaranta idan kayi leti ya ce miyasa kazo leti kai ka isa kacewa head master miyasa yazo leti? ba zai yiyuwa saboda an bashi wani matsayi wanda ba’a baka ba.
Wannan duk duniya kowa ya yarda da wannan ko ka yarda ko kar ka yadda.
Malam ya kara bada misali yace yanzu muna iya tashi daga karatu yace malam daga ina ka fito,? Kai ka isa kace masa daga ina ya fito hakane ko ba haka ba mutane sunka amsa Hakane.
Miyasa gwamnonin mu da shuwagabinmu anka basu dama su sanya jiniya suyi yawo kai ba’a baka dama ba saboda shuwagani ne.
Malam ya kasa kawo misali kamar haka.
Ta yadda a office akwai boss, ta yarda a kamfanin da take aiki akwai boss, in a shagon wani take aiki ta yarda akwai oga, a gidan aure ne babu boss zai yiyu? karya ne karya ne karya ne.
Likitoci ae kuna da kungiyarku yanzu a ma’aikata akwai shugaba idan ya kira taro baka isa kace baza ka zo ba, ka isa umurnin da shugaban ma’aikata ya bayar zaka bayar amma shine a gidan aure za’ayi 50/50, a wace ma’aikata ce da shugaban ma’aikata da ma’aikata akeyi yin 50/50?.
Malam yayi gamsashen bayani akan wannan matsalar tiryan tiryan ka daure ka saura har karshe .
Ga bidiyon nan.
No comments:
Post a Comment