Breaking

Quote of the day

Quote of the Day

Pages

Search here

Friday, 25 August 2023

Atiku Abubakar Uncle dina ne – Ali Nuhu

Fitaccen jarumi nan a Masana’atar Kannywood Ali nuhu wanda shine bakon shirin Gabon Room talk show na wannan sati wanda mutane sun dade suna takon hira fitaccen jarumin.

Ali nuhu dai shima yabi sahun yan uwansa inda ya amshi gayatar wannan dandali inda mai gabatar da shirin ta kanyiwa jarumai tambayoyi da dama akan rayuwasu da iyalisu da al’amuran yau da kullum.


Mai gabatarda shirin Hadiza Gabon tayiwa Ali nuhu tambaya kamar haka.

Gabon : Daddy tambayata a nan shine anzo zaben shugaban kasa sai ka zabi tinubu ba Atiku ba ?

Ali Nuhu: na’am

Gabon : bayan naga Gombe da Adamawa suna kusa da juna miyasa bakayi gida ba ka tsallaka can miya faru ?

Ali Nuhu: kusan bawai gombe da adamawa suna kusa ba Atiku da mahaifina sunyi aiki tare Nigeria acounscience a nan kano suna da wannan dangantakar tare sukayi forming party PDP atiku yayi playing major rule yayi kokari lokacin da PDP take son karba gwamnatanci a gombe yahi playing major rule kuwa was successful so uncle dina ne.

Gabon : sai ka tsala kabar gida.?

Ali Nuhu: a nawa concept dina na siyasa shine wanda abinda kake gani shine mafita shine reality a gareka kuma shine zai ciyarda kasa gaba.

Na farko unclè ne kamar yadda nagayamiki kuma yana daga cikin elders da muke girmamawa a arewa.amma idan mutum ya tsaya ya aje portfolio da irin abubuwan da yayi, ni inason mutumin da yake jan matasa ya basu dama ya jasu ya basu kowace dama a field dinda suke ciki a kamfen media legas.

Gabon : inda an baiwa atiku dama ya zamo shugaban kasa bazai iya jawo matasa ba..?

Ali Nuhu : zai iya amma ni kesan abinda nake gani PDP party ce ta riga tayi mulki a baya kuma a ganina za’a iya dawo da wadannan mutane a cigaba a gwamnatin mu, kuma munsa abinda muka fuskanta irin kura kuran da anka samu zuwa APC na biyu muna tunanin in sha Allahu za’a gyara.


No comments:

Post a Comment